28 Satumba 2016 - 17:41
Wasu Mayakon Boko Haram Yan Kasar Chadi Sun Koma Gida

Wasu kafofin labarai daga kasar Chadi sun bayyana cewa wasu matasa mayakan boko Haram kimani 60 sun bar sansanoninsu da ke Nigeria sun koma gida.

Shafin yanar gizo na Africa Time ya nakalto wata majiya a kasar na Chadi daga garin Lac wanda ke kan iyaka da tarayyar Nigeria, kan cewa wasu matasa kimani 60 tare da mata ukku  wadanda suka kasance tsoffin mayakan boko haram kuma yan garin sun dawo gida a makon da ya gabata.

Gwamnan lardin Lac na kasar ta Chadi Malam Adamu Forteil ya shaidawa mutanen lardin Lac kan cewa kada su ji tsaro don jami'an tsaro suna kula da kai kaiwan wadan nan matasa, don tabbatar da cewa sun bar kungiyar ta Boko Haram da gaske.

Tun shekara ta 2009 ne kungiyar Boko Haram ta fara daukar makami don yakar sojojin tarayyar Nigeria da kuma na makobtanta, wanda sanadiyyar haka akalla sun kashe mutane dubu 20 a cikin wadan nan kasashe. Sannan wasu miliyon biyu da 600 kuma suka zama yan gudun hijira a ciki da wajen kasashensu.288